Yanzu-Yanzu: Jarumar kannywood Maryam Yahaya ta wallafa wata bidiyo a TikTok wanda ta janyo mata cece-kuce

Maryam Yahaya jaruma ce a masana’antar kannywood wacce take sharafinta a wannan lokacin duba da daukakar da tayi a shirin fina-finan na kannywood tun farkon bayyanar ta a wani shiri mai suna Mariya.
Jaruma Maryam Yahaya tajima tana daukar lambobin yabo a shirin fina-finan da take fitowa na masana’antar kannywood, wanda a yanzu kuma tayi sanyi dalilin rashin lafiyar da tayi.
Kamar yadda a kwanakin baya kuka sha jin labarai kala-kala akan rashin lafiyar jaruma Maryam Yahaya wanda ake zaton ko asiri ma aka yiwa jarumar ganin yadda ta daukaka lokaci guda a masana’antar kannywood.
Jarumar tasha wahala sosai kan rashin lafiyar da take inda har wasu basa iya gane ta sabida ramewar da tayi, amma daga karshe angano bakin zaren abin da yake damun jarumar, inda likitoci suka bayyana cewa maleriya ce da tayifot suke yiwa jarumar katutu.
Amma a yanzu Allah ya bawa jarumar Maryam Yahaya lafiya inda har take wallafa wasu sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram tare da wasu bidiyoyin ta.
Sai a yanzu kuma muka sani wata bidiyin jarumar a wata tasha mai suna, Duniyar Kannywood, dake kan manhajar Youtube inda ta wallafa wannan bidiyon nata a dandalin TikTok tana bin wata waka.
Inda a cikin wakar zakuji ana wata magana mai kama da harshen Damo, inda har ma jama’a suka yiwa jarumar cece-kuce akan wannan bidiyon data wallafa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.