Advertising
Advertising
Labarai

Allah ka kare mu: Abubuwan da zasu iya hana mace shiga gidan Aljanna koda tana Sallah da Azumi

A wani labari da muka samu daga shafin jaridar Rariya inda suka wallafa labarin akan matan da suke aikata wasu laifuka wanda ta dalilin kahan mace bazata shiga Aljanna idan ta mutu ko kuwa tana Sallah tana Azumi.

Advertising

Abin da shafin suka wallafa dake cikin balarin gashi kamar haka.

(1) Duk matar da take da aure kuma tayi zina.

(2) Duk matar data mallaki mijinta ta hanyar asiri ko tsafi.

Advertising

(3) Duk matar data hana kishiyarta ta zauna da mijinta lafiya.

(4) Duk matar data raba mijinta da ‘yayan sa ta hanyar asiri ko yaudara.

(5) Duk matar data raba mijinta da ‘yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara.

(6) Duk matar da tayi asiri akan saukarwa da kishiyar jinin haila duk ranar kwananta sai jinin haila yazo mata.

(7) Duk matar da tasa aka daure mahaifar kishiyarta domin karta haihu.

(8) Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta kuma ta tabbatar ba nasa bane.

(9) Duk matar data daure bakin mijinta sabida kar yayi mata kishiya, ma’ana shine duk ranar da zai kwana a dakin kishiyar sai ya zanto ba namiji ba, amma idan ya dawo dakin wanda tayi sishirin sai ya dawo namijin sa.

(10) Duk matar da taba godewa mijinta akan abubuwan da yake mata na alkairi.

(11) Duk matar data nemi mijinta ya sake alhali kuma baya cutar da ita kuma ba yadda ya iya dole sai ya saketan.

(12) Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta.

(13) Duk matar da tabayin wankan janaba bayan ta sadu da mijinta ko batayin wankan haila ko biki

(14) Duk matar da take tona asirin mijinta a cikin kawayenta.

(15) Duk matar da take annamimanci.

Wadannan kadanne daga cikin abubuwan da zasu iya hana mace shiga gidan aljanna ko kuwa tana Sallah da Azumi, don haka ya kamata a kiyaye wadannan abubuwan domin a sami babban rabo a gobe kiyama.

Advertising

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button