Labarai

An kama wasu karuwai da suka yiwa matar aure mummunan duka akan taje otel neman dan iskan mijin ta

Wata matar aure ta sha da kyar a wajan wasu karuwai da sukayi ta bugunta suka mata dukan kawo wuka.

al’amarin ya faru ne a lokacin da matar tahe neman mijinta a wani babba otel wanda yake kusa da tashar mota dake birnin Badun jigar Oyo.

Wata majiya data bayyana yadda labarin yake tace: Wannan matar auren bahaushiya ce ta sami labarin akan mijin ta yana zuwa wani otel yana kwana a dakin karuwai sannan kuma idan ya koma gida sai yayi mata karya da cewa shidimomin kasuwanci ne yasa bai koma gida ba.

Amma da matar tasa taga abin ya yawa sai ta fara zuwa wannan otel din da taji labarin mijin nata yana zuwa, inda take zargin mijin nata da tarewa a dakin wata karuwa bayan kuma ya barta da ‘yaya uku 3 a gida.

Bayan matar taje otel din sai ta tabbatar da labarin da ake bata akan mijin nata yana zuwa otel inda tayi ido biyu da shi yana kwance a dakin wata karuwa, daga nan kuma ta koma gida tana kuka ba tare da tacewa mijin nata komai ba.

Da karuwar taga haka sai ta jawa mijin matar kunne da cewa kar ya kara zuwa wajan ta domin gudun abin da zai faru, sabida bata so fada ya auku a tsakanin sa da matar tasa.

Bayan wannan lokacin sai matar mutumin ta sake kowama wannan otel din bata ga mijin nata a can, bayan zuwan ta sai tayi kokarin saka shi a gaba domin su koma gida amma sai yaki yarda.

Hakan yasa matar tasa hankalin ta tashi ranta ya faci inda ta fusata nan da nan ta fara dukan daya daga cikin wadannan karuwan da suke wajan.

Inda suka kuma karuwan suka mata taron dangi suka fara dukan ta basu kyaleta ba sai da suka lagada mata dan banzan duka.

Daga nan aka kai matar asibiti domin dba lafiyarta da kuma yi mata magani akan raunukan da wadannan karuwan suka yi mata, al’amarin da yakai ga zuwa ofishin ‘yan sanda.

Shugaban tashar sun hanzarta daukar mataki akan wanna abin da karuwan suka aikata sannan kuma an sasanta lamarin ta hanyar yankewa karuwan hukunci aka daukar nauyin biyan kudaden jinyar wannan matar.

Sannan kuma aka ja kunnen mutumin da cewa kada a kara ganin sa a wannan otel din, kuma aka bawa matar tasa hakuri akan abin daya faru, sanann aka umarci matar da suyi sulhu na musamman da mijin nata.

Wannan shine karshe labarin zamuso mu karbi ra’ayoyin ku akan wannan labarin, mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button