Jami’an Hisba jihar kano sun gwabza da mai bindiga a yayin da suke shaye shaye.
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simame wajen filin sauka da tashin Jiragen sama ta jihar, ta kama ‘yan mata da samari a wurin da ake shaya-shayen Giya da kuma aikata badala har aka yi zargin wani jami’in tsaro ya yi barazanar hana kamen.
A dai dai lokacin da jami’an Hisba suka kai simame sai suka ci karo da wani jami’in tsaro ya hana kamen, Inda ya zare bindiga yay ikirarin duk wanda ya matso sai ya harbe shi.
Nan fa Jami’an Hisba sukai charko charko, daga bisani kuma sukai kabbara suka afka musu inda jami’a ya maida bindiga su kuma suka kaman tarin yan mata da samarin masu aikata badala a wajen.
A daran jiya yaran jami’in daya zare bindida suka zo sukai gan gami a bakin kofar hukumar Hisba, har suke yin kurin zasu shiga Hisba ta karfin tuwo amma basu sami damaba.
Daga bisani dai jami’an Hisba sunyi nasarar kama mutumin daya zare bindiga da yarinya sa, An kuma sami wata cikin matan da aka kama na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.
sanimuhammaddargomi@gmail.com