Advertising
Advertising
Labarai

Kada a ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda domin hakan zai haifar da mummunan tashin hankali, cewar Sheukh Ahmad Gumi

Sheikh Ahmad Gumi ya sake jaddada bukatar sa kan cewa ayiwa ‘yan bindiga afuwa sannan kuma a inganta musu rayuwar su.

Advertising

Malam Ahmad Gumi ya jima yana gargadin Gwamnatin tarayya da cewa kada ta kuskura ta ayyana ‘ayn bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Kamar yadda Sheikh Ahmad Gumi ya fadi cewa: Daukar wannan matakin zai iya sa ‘yan bindigar su hada kai da ‘yan Boko Haram da kungiyar ISWAP, wanda hakan zai iya jefa jama’ar Arewa cikin mummunan yanayi.

Malamin ya kara da cewa: Yiwa ‘yan bindiga afuwa zai kawo karshen zubar da jinin mutane a Arewa, sannan kuma yace ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda zai sake haifar da wasu matsaloli na ta’addanci.

Advertising

Sheikh Ahmad Gumi yayi wannan furuci ne a lokacin da ake sanya marayu sukuni na uku 3 a shirin samar musu da ilimi da kuma kula da lafiyar su wanda gidauniyar musulinci a Kawo ta dauki nauyin shiryawa.

Malamin ya shawarci Gwamnatin tarayya dake karkashin jagorancin shugaba Muhammad Buhari da cewa, kada ta zama silar karin kashe-kashen mutane.

Sheikh Ahmad Gumi ya kara da cewa: Idan har akwai wata hanya da zata dakatar da zubat da jini, zai fi kyautuwa ayiwa ‘yan bindigar kwatankwacin abin da akayiwa mayakan Niger Delta.

Wanda sun kasance suna fasa bubutun mai da kuma zubar da jinin mutane amma a shirye suke da su ajiye makaman su idan har za’a yi musu afuwa da daukar nauyin su, yace inaga za’a iya yiwa ‘yan bindiga haka.

Ya kara da cewa: Mungana da ‘yan bindiga kuma a shirye suka da su ajiye makaman su, amma idan su dai na kuma ba’a samar musu da ilima ba da kudin da zasu kula da kan su, to tabbas zasu koma gidan jiya.

Idan ake ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda to za’a haifar da wata matsalar su masu laifi ne ba masu bukatar komai ba, idan aka mai da su kamar ISAWP Ko Boko Haram to zasu iya hada kai da su.

Dole ne a kula wajan magance masu laifi kuma jahilai domin zamu yake su da makami idan akwai bukatar hakan, amma a yanzu sulhu shine yafi alkairi.

To masu sauraran mu zamu so mu karbi ra’ayoyin ku akan wannan bayani da Sheikh Ahmad Gumi yayi akan cewa, kada a ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Advertising

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button