Sheikh Sudais ya samar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa tare da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon Allah S.A.W
Kasar Saudiyya ta samar da wani mutum-mutumi na zamani a Masallacin Harami a ranar Larabar da ta gabata, shugaban kula da al’amuran Masallacin, Sheikh Dr, Abdulrahman Bin Abdulaziz Al-Sudais, shine ya kaddamar da mutum-mutumin.
An bayyana cewa mutum-mutumin an yi shi ne da fasahar zamani zai iya daukar ruwa mai yawan lita 68, kuma zai iya shafe awa hudu cur yana aiki tare da zagaye wuri mai nisan mita 2,000 a kowacce sa’a daya.
Kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, Dr, Al-Sudais ya bayyana cewa, ma’aikatarsa tana kokari wajen aiki da bayyana abubuwan dake wakana, hakan kuma na da nasaba da kokari da yake na gabatar da fasaha a manyan Masallatan guda biyu 2 da za su yi daidai da zamani.
Hukumar Masallatan ta kara da cewa, za ta yi kokari wajen tabbatar da cewa duka Mahajjata da masu zuwa Umara sun samu tarbar da ta dace da zarar sun sanya kafar su a cikin Masallatan guda biyu 2.
Sannan kuma ana fatan ta hanyar samar da kwarewa mafi kyau, aikin hukumar Masallatan guda biyu 2 zai iya kawo martaba da wayewa ta masarautar wajen hidimar da ake yiwa Masallatan guda biyu 2 masu alfarma da alhazansu.
Haka kuma Dr, Al-Sudais bai manta da yaba ayyukan na’urorin mutum-mutumi na zamani ba da aka yi da kuma rawar da suke takawa wajen inganta tsarin hidimar da ake ba wa maziyartan Masallatan guda biyu bisa sabbin ka’idojin kasa da kasa.
Masarautar dake kasar Saudiyya tabbas tana samun cigaba sosai tare da amfani da fasahar zamani don saukaka ibadar maziyarta da mahajjata da suke zuwa aikin Hajji da Umara, da kuma cigaba da bin matakan kariya akan yaduwar annobar cutar COVID-19.
Daya daga cikin amfanin da mutum-mutumin zamanin zai yi wajen inganta ayyukan Masallatan guda biyu 2 dake da ban sha’awa shine, na’urorin za su dinga rabawa Mahajjata ruwan Zamzam wanda hakan zai taimaka wajen hana yaduwar cutar annobar COVID-19 a tsakanin alhazai, kamar yadda jaridar Labarunhausa ta tattara wadannan bayanan.