Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Shin wai yaushe jaruma Rahama Sadau zata daina sanya irin wadannan kayan kalli wasu hotuna data wallafa sanye da kayan

A ‘yan kwanakin nan jaruma Rahama Sadau ta firgice wajan wallafa zafafan hotunan ta kala-kala a shafin ta na sada zumunta Instagram, tun bayan dawowarta daga kasar India.

Advertising

Rahama Sadau ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood da wanda take taka rawar gani duba da yadda take rayuwar ta gaba gadi babu mai taka mata birki.

A yanzu jarumar ta fitar da wani sabon salo wanda hakan yasa jama’a suke mamakin abin duba da yadda take shigar kaya kala-kala kamar dama ba ‘yar kasar Nageriya bace.

Tun bayan da jaruma Rahama Sadau ta dawo daga kasar india take nuna wasu sabbin halaye wanda ada ba sosai take nunawa ba, a yanzu jarumar ko hotuna zata dauka babu ruwanta da sai ta sanya dankwali a kanta.

Advertising

Haka ake daukar ta hoton ba tare da jin kunya ba ko kuma ganin ita ‘yar musulmai ce ba, dama kayan da take sanya kuwa ba’a maganar su domin wannan ba bakwan abu bane a wajan ta.

A yau kuma jarumar ta sake wallafa wasu sabbin hotunan ta a shafin nata na sada zumunta wato Insragram, inda zaku hotunan nata ta daujesu ne da wasu matsatstsun kaya kamar ba ‘yar hausawa ba.

Ga hotunan nata domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button