Labarai
Subahanallah: Wani ginan beni mai hawa 25 ya rushe tare da mutane a ciki da yayi sanadiyar mutuwar su
Kamar yadda shafin BBC Hausa suka wallafa hotunan wani ginin beni mai hawa 25 da yayi sanadiyar mutuwar jama’a da dama a jihar Legas.
Advertising
Mun sami rahoton faruwar lamarin a shafin BBC Hausa tare da hotunan benin mai hawa 25, kamar yadda rahoton nasu ya fara da cewa.
Wani beni mai hawa 25 da ake ginin sa a birnin Ikkon dake jihar Legas ya rushe tare da binne mutane wanda yayi sanafiyar mutuwar su.
Lamarin ya faru ne a unguwar Ikoyi a ranar Litinin kamar yadda jami’an da suke ceton al’umma suka sanar, wanda har yanzu babu tabbas akan yawan mutanen da ginin benin ya rufta da su.
Advertising
Amma an sami ma’aikata da kuma jama’ar dake makwaftan yankin suna tonowa mutanen da wannan ginin benin ya rufta da su.
Ga hotunan nan domin ku kalla.
Advertising