Advertising
Advertising
Labarai

Budurwar da tafadi mummunar magana akan malamai wani matashi ya mata wakin babban bargo

Kamar yadda kuka ji labarin wata budurwa wanda taci mutuncin malamai tare da fada musu mummunar magana, dalilin sheikh Abdallah Gadon kaya yayi nasiha ga maza idan zasu auri su tabbatar da tayi jinin al’ada kafin ayi auren.

Advertising

Bayan malamin yayi wannan nasihar sai budurwar ta wallafa wata bidiyo a manhajar TikTok inda take martani ga malamin tana fadan wasu maganganu marasa dadi, wanda har jama’a suke ganin abin da tayi bai dace ba.

Wanda budurwar take fadin cewa, ai suma malaman suna neman ‘yayan mutane ma’ana abin da take nufi shine, malaman suna bibiyar mata domin suyi lalata da su tun da tace malaman suna neman ‘yayan mutane.

Bayan wannan al’amarin ya faru sai kuma a yau muka sami wata bidiyon wanda tashar, Murna hausa top Tv suka wallafa a tashar su dake kan manhajar Youtube.

Advertising

Inda wani matashi ya bayyana a cikin bidiyo yana maida martani ga wannan budurwar data fadi wannan mummunar magana ga malaman, inda matashin ya nuna rashin jin dadin sa ga abin data aikata.

Ya yimata wankin babban bargo tare da fada mata maganganun da zasu ratsa ta domin tasan ta aikata kuskure, kamar yadda zakuga matashin a cikin bidiyon da zamu nuna muku a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/3mVsWnKKQvk

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button