Labarai

Shahararran malamin addinin musulinci yayi bayani akan azabar da za’a yiwa mata masu karin gashi

A wata bidiyo da muka samu ta malam Aminu Daurawa wanda yake bayani akan matan da suke karin gashi da kuma masifar da zasu fuskan ta.

Kamar yadda kuka sani yawancin mata suka bukata suga gashin kansu ya tswo da yawan da kowa zai na sha’awar sa musammam ma a bangaren maza, domin suna bukatar mace mai yalwar gashi.

Sai dai kuma akwai matan da suke aikata abubuwan da zasu iya kaisu ga halaka ta dalilin neman yalwar gashin, domin wasu matan suba bin hanyoyin da basu dace ba domin ganin gashin kansu yayi yadda suke bukata.

Hakan yasa mata da yawa sukan zake akan abin da Allah bai nufesu da shi ba kamar kyawun fuska yalwar gashi da dai sauran su, musammam ga ‘yam matan yanzu wasu suna karin gashi wasu kuma suna sauya launin fatar jikin su ta hanyar yin bilitin.

Wanda hakan haramun ne ga duk matar da take aikata wadannan abubuwan domin addinin musulinci bai yarda da hakan ba, sannan kuma bama ga ‘yam mata ba akan samu wasu matan auren da suke aikata irin wadannan abubuwan na karin gashi ko bilitin.

Amma abin da malamin yake nufi anan shine matan da suke karin gashi da da gashin dabbobi domin gashin nasu yayi yawa to hakan haramun ne a addinin musulinci.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin malamin.

https://youtu.be/Y5LHCO_hJ88

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button