‘Yan bindiga sun kai hari makarantar jami’a dake babban birnin tarayya Abuja domin su kwashe Dalibai
Alamu suna nuna cewa tsaro a kasar Nageriya yana nema ya zama irin abin da hausawa suke cewa, wata miyar sai dai ayi ta a makota, ma’ana shine tsaro a Nageriya sai dai a gani a wasu kasashen.
Sabida alamomin suna nuna cewa wannan matsalar tsaron ta kasar Nageriya tana neman tafi karfin Gwamnatin kasar, sakamakon har yanzu matsalar taki ci taki cinye wa.
Kamar yadda Dalibai a kasar Nageriya suka zama kamar namun dajin da mafarauta suke harin su ako da yaushe, wato kamar yadda mafarautar suke kaiwa namun dajin hari haka ‘yan bindiga suke kaiwa harin su makarantu domin su kwashe Dalibai.
‘Yan bindigar suna kaiwa harin nasu tun daga makarantar Pramary, Secondary da Jami’a domin su kwashe Daliban suyi awon gaba da su.
To a yanzu wani saban labari ya bayyana yadda ‘yan bindigar suka kai wawaso ga makarantar jami’a dake babban birnin tarayya na Nageriya Abuja, kamar yadda BBC Huasa suka kawo cikekken rahoton.
Kalli wannan bidyon dake kasa domin kaji cikekken labari.
Wonderful