Jami’an tsaro sun kama wani alaramma wanda yake koyar da almajirai karatu yayi garkuwa da dan kanin mahaifin sa
Kamar yadda kuka sani wannan rayuwar tamu ta yanzu al’amura sun lalace sannan rashin kudi ya yiwa al’amma katutu, wanda ta dalilin haka ake yawan sace-sace da bin hanyoyin da mutum zai raunana addinin sa domin ya sami kudi.
Matsalar tsaro da yin garkuwa da mutane a Nageriya ya maza ruwan dare duba da yadda rashin kudi da rashin aikin yi ya yiwa matasan kasar yawa, wanda hakan yasa wasu daga cikin su suke bin duk wata hanya da zasu sami kudi mai kyua ko marar kyau.
Yanzu zakaji labarin cewa an sace mutum sannan kuma ana bukatar wasu kudade masu yawan gaske kafin a sako mutum, wanda wannan kudin da za’a bada wani koda zaka kashe shi bazai iya nemo wannan kudin ba.
Sannan kuma sai kaji labarin wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kananan kauyuka sunyu farnar da ba’a zato sannan kuma su debe dukiyoyin al’ummar garin, kama daga dabbobin su da duk wani abu da zai amfane su.
To a yau kuma mun sami labarin wani alaramma wanda yake koyar da almajirai karatu tamka wani babban laifi wanda daga karshe asirin sa ya tonu, aka kamashi da laifin yin garkuwa da dan kanin baban sa.
Alaramman yayi garkuwa da dan kanin baban nasa ne domin ya sami kudaden da zai na amfani da su wajan bina bukatun kansa, sannan kuma wani abin mamaki shine yadda yake fadin littatafan da yake karantawa najin tsoron Allah.
Bayan yayi garkuwa da dan kanin baban nasa sai dubun sa ta cika inda hukumomin tsaro dake jihar Katsina suka kama shi, suka tara ‘yan jarida da manema labarai akan nasarar da sukayi wajan kama masu garkuwa da mutane.
Inda ake zargin shima alaramman mai suna Jamilu Idris mai shekaru 39 mazauni a sabin Fegi dake kauyen ‘yan kara a karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina.
Yaje har gidan su yaron wanda yake dan kanin babansa ne inda ya kama hannun yaron ya tafi da shi har zuwa wani waje mai suna Dustins Alhaji dake garin Abuja.
Bayan alaramman ya dawo garin su dake jihar Katsina sai ya kira mahaifin yaron yake sanar da shi cewa, ya kawo naira Miliyan biyar domin ya karbi dan sa, kamar yadda zakuji daga bakin alaramman a cikin bidiyon dake kasa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin alaramman.