Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ko Producer yana lalata da mace kafin ya sakata a fim din sa to ni bazan bada kaina ba, cewar jaruma Bilkisu Abdullahi

Kamar yadda kuka sani ‘yan jarida suna yawan yin shira da jaruman masana’antar kannywood akan abin daya shafi rayuwar su da kuma sana’ar su ta harkar fim.

Advertising

Kamar jaridar BBC Hausa dama sunfi kowane gidan jarida yin shira da jaruman na kannywood wanda har suka fitar da sashen shira mai suna, Na daga bakin mai ita.

To a wannan lokacin ma wata jarumar kannywood mai suna Bilkisu Abdullahi ta amsa wasu tambayoyi a yayin da take shira da ‘ya jarida, kamar yadda wata tasha mai suna, Top Hausa ta wallafa labarin shirar da akayi da jarumar.

Jaruma Bilkisu Abdullahi ta kasance ‘yar asalin kabilar fulanin adamawa wanda ta taka rawar gani a shirin fina-finan masana’antar kannywood, ta amsa wasu tambayoyi da aka mata a lokacin da take shira da ‘yan jarida.

Advertising

A lokacin da yake shira da jarumar ta bada wata amsa wanda jama’a sukayi mamakin wannan amsar data bada, inda take cewa, bazan iya bayar da kaina ga Producer ko kuma Director yayi lalata dani ba domin ya sakani a cikin fim din sa.

Wannan amsar da jarumar ta bada jama’a sunyi mamaki matuka inda suke tunanin dama sai mace ta bada kanta sannan za’a sanya ta a cikin shirin fim.

Amma kafin ta bada wannan amsar anyi mata wasu tambayoyi akan matan da rayuwar take lalacewa kafin su shiga harkar fim, sannan kuma aka tambaye ta da cewa ko kema hakan ya taba faruwa a kan ki,

Sai jarumar tace: Ko Producer yana lalata da mace kafin ya saka ta a fim to ni bazan yarda ba, domin bazan taba bayar da kaina ga wani namiji ba idan ba mijina na sunnah ba.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken labari.

https://youtu.be/GeXA2oQQgC4

Advertising

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button