Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jarumar kannywood Uwar marayu wato Hadiza gabon ta ciyar da almajirai tare da biya musu kudin sabon fim din nan Fanan na Mansurah Isah

Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah kamar yadda kuka sani ta fitar da wani sabon fim din ta mai suna Fanan wanda ya samu karbuwa a wajan al’umma, wanda har jarumar take cika baki akan fim din.

Advertising

Inda Mansurah Isah take cewa, wannan fim din nata na Fanan ya kafa tarihi a masana’antar kannywood duba da daukakar daya samu lokaci guda, a zaton da wasu mutanen sukayi akan wannan maganar da jarumar tayi shine.

Babu wani fim a masana’antar kannywood da aka taba haskaka shi ya sami daukak kamar sabon fim din ta Fanan, domin al’umma sun karbe shi hannu biyu sannan kuma ta sami kudade masu yawa a lokacin da aka haska fim din.

Bayan haskaka fim din nata abokanta da masoya na kusa da ita sun bada gudunmawar su ga sabon fim din nata duba da yadda fim din ya burge duk wani mai kallon shirin fim na huasa.

Advertising

A yau kuma mun sami wata bidiyo da jarumar masana’antar kannywood HadIza gabon wacce akewa lakabi da uwar marayu, ta gayyaci wasu almajirai wajan haskaka fim din Fanan tare da biya musu kudin shiga, sannan kuma ta ciyar dasu abinci kala-kala da abin sha.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/FNyf6sf34qE

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button