LABARINA SEASON 4 EPISODE 5
Ga masu kallon shirin LABARINA mai dogon zango wanda tashar Saira Movies da Arewa24 suke haskawa a duk sati, sun san cewa a wancan satin da yawuce shirin ya kare da wajan da Mahmud ya fadi yana wasu abubuwa kamar zai mutu.
Amma dalilin da yasa Mahmud ya shiga wannan halin shine, bayan Sumayya ta masa taimako kala-kala wanda har ta kai ga kowa yana tunanin kamar soyayyar su zata dawo kamar yadda suke a baya.
To amma sai al’amarin ya sauya Ita Sumayya tana masa wannan taimakon ne domin domin halabrcin da yamata a baya lokacin da tafada cikin wani hali mai wuyan bullewa wanda alokacin tana bukatar taimako.
Bayan wannan taimakon da yamata sai ita ma a yanzu take kokarin saka masa da irin taimakon da yamata shine ake tunanin ko soyayyar su ce zata dawo.
To bisa mamaki a shirin na satin baya da yawuce sai Mahmud yake bayyanawa Sumayya abin da yake ransa wanda tun dawowar sa gareta yake son bayyana mata amma bai sami dama ba sai a wannan lokacin.
Bayan Mahmud ya bayyana mata abin da yake ransa yana bukatar Sumayya ta karfi soyayyar su koma kamar yadda suke a baya, amma sai Sumayya ta bayyana masa cewa ita a yanzu bata san a kawai dai tana taimakonsa ne kamar yadda shima ya taimaketa a baya.
Wannan dalilin yasa Mahmud ya fadi kasa yake shure-shure kamar zai mutu bayan Sumayya ta fita daga office din nata.
Tun daga wannan lokacin jama’a suke dakon shirin na zangon gaba watio na wannan satin wanda za’a haska shi a yau, domin kowa yana tunanin Mahmud zai iya mutuwa a cikin shirin.
A wancan satin shirin ya kare a zango na 4 fita ta 4 wanda a turance ake kira da Season 4 Episode 4.
To a yau kuma zasu haska muku zango na 4 fita ta 5 wato Season 4 Episode 5.
Ga shirin fim din nan domin ku kalla: LABARINA SEASON 4 EPISODE 5