Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Sana’ar fim itace silar daukakata a rayuwa da duk wani abu dana mallaka na jin dadin rayuwa, cewar Sani Musa Danja

Ficaccan jarumin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, Sani Musa Danja, ya bayyana cewa, harkar siyasa da yake da wasu kasuwancin sa bazasu hana shi fitowa a shirin fim ba.

Advertising

Jarumi Sani danja ya fadi hakane a lokacin da wasu tattauna da jaridar Damukaradiyya akan maganar da ake cewa, a yanzu jarumi Sani danja yafi mayar da hankalin sa kan harkokin siyasa fiye da harkar fim duba da yadda aka san shi da harkar tun asali.

Jarumi Sani danja ya fadi cewa: Duk wanda ya sanni da harkar fim ya sanni kuma ta dalilin harkar duniya ta sanni kana duk wani abu ra rayuwa dana mallaka da dalilin harkar fim na samu, don haka babu yadda za’ayi na bar harkar fim.

Sani danja ya kara fadin cewa: Ko ita siyasar sai da nafito a harkar fim sani suna sannan na sami damar shiga siyasa a lokacin mulkin Jonathan, wanda a wannan lokacin mutane suka fashimci na shiga harkar siyasa sosai.

Advertising

Ya kara da cewa: Kuma bayan harkar siyasa dana shiga ai ina yiwa kamfanonuwa talla kamar Glo da sauran manya-manyan kamfanonuwa da kungiyoyin duniya, duk wadannan basu sa na daina harkar fim ba domin harkar fim sana’ace da aka sanni da ita sabida haka babu yadda za’ayi na daina harkar fim.

Daga karshe jarumi Sani danja yayi kira ga gwamnati akan ta bayar da goyon baya ga masu harkar fim sabida harkace da miliyoyin mutane suke samin aikin yi a cikin ta, wanda hakan zai bawa mutane dama su sami aiki ba sai sunyi zaman jiran aiki ya fito musu ba.

Muna bukatar ra’ayoyin ku akan wannan labarin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button