Advertising
Advertising
Uncategory

Mahaifiya ta da ‘yayana 4 tare da ‘yan uwana 4 duk sun kone kurmus a cikin motar da ‘yan Bindiga suka sawa wuta, inji Matar data sha da kyar

Wata Mata data tsallake rijiya da baya a harin da ‘Yan Bindiga da suka kai wa motar has a ranar Litinin Gidan Bawa a karamar hukumar Isa ta Jihar Sokoto, a halin yamzu rayuwarta ta sauya zuwa mafi muni sakamakon harin da aka kai musu.

Advertising

Matar ‘Yar Sabon Birni mai kimanin shekara 48 mai suna Shafa’atu wacce kusan dukkan jikinta ya kone, tana jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

Daily Star Nigeria ta ziyarce Matar inda ta bada Iabarin irin halin data shiga inda take bayyana cewa, Muna cikin motar bas mun kasance mu talatin da uku ne manya 33 da kuma sauran fasinjojin duk yara ne kwatsam sai ga ‘Yan Bindigar suka zo suka fara harbin motar mu, Motar bas ta taso sai kawai na tsinci kaina a kasa da ina konewa.

Matar tace: ‘Yayana mata 3 da yaro na dan watanni 10
sun kone a bayana mahaifiyata da ’yar uwata kanena, kani na na kusa da kanin mahaifiyata duk sun kone a cikin motar.

Advertising

Ni da wani mutum mun tsere ta hanyar mu’ujiza amma mutumin daga baya ya mutu sakamakon harbin sa da aka yi da bindiga.

Yaro na yana bayana amma shi ma ya kone, sauran ‘yaya na mata uku duk sun girma kuma na rasa su duka inda take wannan bayanin cikin raunin murya, Shafa’atu tace daya daga cikin ‘yayan ta da iyayen ta suka rasu a baya aka kawo wa mahaifiyarta kulawa, ita ma an kona ta tare da mahaifiyarta.

Baza ku iya tunanin abin da na keji ba Iokacin da kike matsayinki na uwa kina kallon ‘yayanki da mahaifiyarki da wasu ‘yan uwanki guda hudu da kuke dariya tare, suna kone kuma babu wani abu da za ku iya yi game da shi.

Kawun mahaifiyar Shafa’atu wanda aka bayyana sunansa da Muhammadu amma ba sunan gaskiya ba wanda ke kula da Shafa’atu a asibiti, yace ya halarci jana’izar mamatan.

Muhammadu ya bayyana wace: A halin da suke ciki ya wuce tunani sai dai imani da cewa abu ne mai zafi daba shi da zafi domin bama san abin da zamu ji ba.

A halin da ake ciki a yanzu, kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Sokoto Kamaldeen Okunola wanda ya bayyanawa manema Iabarai bayan ganawar sirri da Gwamna Tambuwal a ranar Laraba ya fadi cewa.

Jimillar mutanen dake cikin motar bas da ‘Yan Bindigar suka harbe har Iahira su 23 sun mutu sakamakon gobara data tashi yayin da mutane shida suka sami raunuka, masu kananan raunukan kuma suna karbar magani a asibiti.

Ba a ga Shafa’atu da sauran wadanda suka tsira daga lamarin da ya faruba a lokacin da Daily Star Nigeria ta zanta da wasu mutane wanda suka ju kananan raunuka.

Shafa‘atu dai sama da kashi 60% na jikinta ya kone kuma ana shirin karkatar da abd zuwa sashin kula da Iafiya na Asibitin, yayin da wani mutum a asibitin Sabon Birni ya samu mummunar kuna a kafar sa daya tare da wasu sassan jikin sa.

A yanzu haka Ana dai tada jijiyoyin wuya a Jihat Sokoto tare da Jihohi da dama kan lamarin, sakamakon rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Advertising

232 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button