Labarai

Yanzu-Yanzu: Wata Kotu dake jihar Kano ta bada umarnin kama dan wasan barkwanci Shagirgirbau kan wani laifi daya aikata

Kamar yadda kowa yasan dan wasan barkwancin nan mai suna Shagirgirbau wanda yake harkar Comedy, ya aikata wani laifi wanda aka bada umarnin kama shi sannan kuma a tsare shi a wata Kotu dake jihar Kano.

Kamar yadda shafin Northern Vine suna wallafa a shafin su na Instagram cewa: Kotu ta bada umarnin tsare mai barkwanci Shagirgibau kan zargin batancin da yayi daga Sultan Ismail jihar Kano.

Wata kotu dake jihar Kano ta bada umarnin maka dan wasan barkwancin nan Shagirgirbau wanda yake wallafa bidiyoyin nasa a kafafan sada zumunta na soshiyal midiya, wanda yake abubuwan barkwanci a cikin bidiyoyin nasa har ma ya sami samoya da dama.

Kotun ta bada umarni a tsare shi har zuwa ranar takwas 8 ga wannan watan da muke ciki, bayan nan kuma za’ayi zama na sauraran karar sa da Gwamnatin jihar Kano tayi.

Bayan wata bidiyo ta Shagirgirbau ya wallafa wanda Gwamnatin tayi zargin cewa, yayi wannan bidiyon ne ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar ganduje da wasu mukarraban Gwamnatin guda biyu 2.

Bidiyon da dan wasan barkwancin yayi wato Shagirgirbau ta karade duk wata kafa ta sada zumunta ta soshiyal midiya, wanda a cikin bidiyon yake fadin cewa a dai na kiransa da “Mista Man”.

Zaku iya kallon wannan biduyon da kuka ajiye muku a kasa domin kuji sauran bayani a cikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button