Jaruma Hadiza gabon bayyana wasu al’amura da suka shafi rayuwarta da iyayanta a shirar da tayi da ‘yan jarida
A wani faifai bidiyo da muka samu wanda ake shira da jarumar masana’antar kannywood Hadiza Aliyu gabon wacce aka sani da Hadiza gabon, ta bayyana wasu al’amura da suka shafi rayuwar ta da kuma asalin kasar da aka haifeta.
Jarumar tayi shira da gidan jaridar kasar Amurka inda yake bayyana cewa, Iyayan ta suna kasance ‘yan Nageriya a wata jiha mai suna Adamawa wanda a can suke da zama.
Sannan ta kara da cewa: Asalinta Bafulatana ce ta fara zamanta ne a gidan wata mata dake jihar Kaduna wanda akewa matar lakabi da uwar marayu, sabida tana rike da marayu sun kai guda 100 a gidan nata.
A cikin wannan shirar da aka tattauna da jarumar an sake tambayarta shin mai yasa yawancin ‘yam fim suke tafiya kasashe daban-daban.
Nan take sai jarumar Hadiza gabon ta bada amsa da cewa, itama tazo daga wata kasar zuwa Nageriya sabida haka dama tun tana ‘yar karama take sha’awar yin tafiye tafiye zuwa wasu kasashen.
Dan jaridar yayiwa jaruma Hadiza gabon tambayoyi sosai akan a abubuwan da suka shafi rayuwar da kuma yadda iyayan ta suka goya mata baya akan shiga harkar fina-finan Hausa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin jaruma Hadiza gabon a shirar da tayi da gidan jaridaf Amurka.