Advertising
Advertising
Labarai

An gurfanar da matar Abdulmalik Tanko wanda ya yiwa Hanifa kisan gilla a gaban kotu domin girbar abin data shuka

A jiya Alhamis rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da Jamila Muhammad Sani matar Abdulmalik Tanko mutumin da yayi garkuwa da Hanifa Abubakar sannan kuma ya kashe ta.

Advertising

An gurfanar da ita a gaban kotun Majistare mai lamba goma sha biyu 12, karkashin mai shari’a Muhammad Jibril wanda take zaune a gidan Murtala.

Lamido Abba Soron Dinki wanda shine mai gabatar da karan kuma lauyan gwamnati tare da rakiyar barista Maryam Jibril, da barista Hafsat Kabir da kuma barista Hafsat Adda’u, ya roki kotu data karantowa wanda ake tuhumar wato Jamila Muhammad Sani matar Abdulmalik Tanko.

Jami’in kotun ya karantowa Jamila tuhumar da ake mata wadda ta kunshi boye Hanifa da kuma tanadar da wajen da aka sace ta, har ta kwashe kwanaki biyar a gidanta.

Advertising

Sai dai kuma Jamila Muhammad Sani ta musanta zargin da ake mata nan take, ta kuma nemi damar yin magana amma kotu ba ta amince da bukatar ta ba.

Da ga nan ne sai mai gabatar da kara ya roki kotu da ta basu wata ranar domin sake gabatar da ita, yayin da kotun ta sanya ranar 2/2/2022, ta kuma umarci a mayar da ita wajen jami’an tsaro ba gidan gyaran hali ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button