Advertising
Advertising
Labarai

Yanzu-Yanzu: Bidiyon da tasa aka kama Shagirgirbau kan wata magana da yafada ga Gwamnan Kano ta bayyana

Kamar yadda kuka sani a jiya ne muka kawo wallafa muku labarin yadda aka kama ficaccan dan wasan barkwanci mai suna Shagirgirbau akan wani laifi daya aikata ake zargin da Gwamnan Kano yake.

Advertising

Inda a lokacin kotu ta bada damar kama shi sannan kuma a tsare shi har tsawon kwana takwas ga wannan watan da muke ciki, domin za’a saurari karar da Gwamnatin tayi a kan sa.

Sai a yau muka sami faifai bidiyon da yayi silar kama dan wasan barkwancin wato Shagirgirbau, inda wannan bidiyon ta karade shafukan sada zumunta na soshiyal midiya kamar su, Facebook, Youtube, da dai sauransu.

Dan wasan barkwancin ya jima yana bawa jama’a nishadi a cikin bidiyoyin da yake wallafa tun lokacin farkon bayyanar sa har kawo yanzu, wanda ada din ba kowane ya san shi ba tun yana abin nasa kamar hauka har ta kai ga jama’a suna jansa a jiki domin ya basu nishadi.

Advertising

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji abubuwan da dan wasan barkwancin yake fada a cikin bidiyon har ta kai ga anyi ram da shi, sannan kuma aka turashi gidan zyaran hali.

Kalli bidiyon kai tsaye.

https://youtu.be/3VJ9cObXnMA

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button