Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

An bayyana wani sabon al’amari akan jaruman kannywood mata da duka shiga harkar fim bayan auren su ya mutu

Kamar yadda kuka sani kannywood masana’anta ce wanda take al’umma masu yawa a cikin ta da ake musu lakabi da jarumai, a cikin jaruman akwai jarumai maza sannan kuma akwai jarumai mata.

Advertising

Daga cikin jarumai matan wasu ‘yam mata ne wasu kuma zaurawa ne wanda ake shirin fim din dasu a masana’anyar ta kannywood, duba da yadda masana’antar tana bukatar manyan mata da kuma matasa.

Wasu daga cikin jarumai matan sukanyi aure kafin su shiga harkar fim wasu kuma sai sun shiga harkar sannan daga baya su nemi auren.

Amma abin dake faruwa shine da yawa daga cikin matan da suke shiga harkar fim bayan auren su ya mutu, to babu tabbacin su sake yin wani auren a gaba sabida kudin da suke samu a harkar bazai barsu sake wani auren ba.

Advertising

Hakama matan da suka shiga harmar kafin suyi aure sukan zauna su mike kafafu ko maganar auren basa sawa a gaban su balle ma suyi ganin sun shiga gidan mazajen auren su, wanda yanzu haka matan kannywood din ko nunanin auren basa yi.

A wannan lokacin kuma mun sami wani faifai bidiyo wanda tashar Gaskiya24 Tv ta wallafa, a cikin bidiyon anyi wani sharhi akan jaruman kannywood mata da suka shiga harkar fim bayan auren su ya mutu.

Inda aka jero jaruman daya bayan daya ana bayani akan su kamar yadda zaku gani a cikin bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button