Jaruma Rahama MK ta shirin Kwana casa’in matar Bawa Maikada tayi auren sirri ba tare da sanin mutane ba
A lokacin da jama’a masu kallon shirin Kwana Casa’in mai dogon zango wanda tashar Arewa24 take haskawa a duk mako, suna tunanin ya zata kaya game da auren jaruma Rahama MK matar Bawa Maikada a cikin shirin sai gashi jarumar tayi aure cikin sirri wanda ba kowane ya sani ba.
Sabida a cikin wannan watan da muke ciki a safiyar ranar Asabar data gabata aka daura auren jaruma Rahama MK da Angon nata a gidan su dake birnin jihar Kano, inda aka daura auren nasu cikin sirri babu wanda ya sani.
Tun farko dama jarumar tana shirin yin aure to amma bata bayyana ba kawai sai labari aka ji jarumar tayi aure, lokacin da wakilin jaridar Damukaradiyya ya nemi jin ta bakin jarumar a wayar Tarho, jarumar ta tabbatar masa da maganar auren inda ta bayyana cewa.
kamar yadda na fada maka kwana uku da suka wuce zan yi aure a wannan ranar, Kuma ga shi Allah ya cika min buri na, Kuma fatan da nake da shi Allah ya sa na samu haihuwa Kuma na mutu a dakin mijina.
Dangane da fim kuwa jarumar ta bayyana cewa: Zata cigaba da fitowa a cikin Shirin Kwana Casa’in mai dogon zango, sai dai Kuma sauran fina-finai ne babu tabbas ta bayyana a ciki.
Ga hotunan jarumar nan domin ku kalla.
Allah yaba da zaman lafiya
Allah ya Basu zaman lafia.