Advertising
Advertising
Labarai

Jarumar Hollywood ta Amurka ta kira wasu kasashen musulmai jahilai dalilin sunki amincewa a haska fim dinta wanda ake nuna auren jinsi a ciki

Kamar yadda kuka sani auren jinsi rahamun ne da yawa daga cikin kasashen musulmai kamar su, Saudiyya, Qatar, Kuwaita da dai sauran su, hukumomin face fina-finai na kasashen suna bukatar a dunga yanke wasu wurare da ake nuna auren jinsi a fim kafim a haska shi.

Advertising

Wani fim da kamfanin Marvel suka fara haska shi mai suna, Enternal, shine fim na farko da kamfanin Marvel suka fara haska shi wanda a ciki ne nuna auren jinsi.

Ficacciyar jarumar Hollywood mai suna, Angelina Jolie, ta caccaki wasu daga cikin kasashen musulmai sabida sun hana haska wani fim din ta da suka shirya shi a kwanan nan, wanda a cikin fim din ake nuna auren jinsi.

Angelina Jolie ta kira kasashen musulman da jahilai dalilin basu amince da haskaka wannan sabon fim din nata ba na kamfanin Marvel, sabida an baga goyon baya wajan na yin auren jinsi a cikin fim din.

Advertising

A cikin fim din nata ana nuna yadda wasu mutane ‘yan jinsi daya suke sumbatar junan su, daga nan kuma sai aka dakatar da haska fim din a kasashen musulmai da suka hada da, Saudiyya, Kuwait, Qatar, Bahrain, Oman.

A kwanakin baya-bayan nan da suka wuce wata hukumar tace fina-finai ta bukaci kamfanin Marvel daya yanke wasu wurare da ake nuna abubuwan da basu dace ba a cikin fim din, amma sai kamfanin ya watsar da wannan umarnin da aka bashi.

Kamar yadda Labarun Hausa da Nbcnews suka ruwauto cewa: Jarumar Hollywood Angelina Jolie wacce ta fito a matsayin Thena Abadi a cikin fim din, ta tofa albarkanin bakin ta akan lamarin a wata shira da akayi da ita.

Jarumar ta kira lamarin marar dadi sannan kuma ta kira wasu kasashen musulmai da jahilai sabida sunki amincewa a haska wannan fim din nata.

Zaku iya ajiyewa ra’ayoyin ku a sashin mu na cokaci akan wannan labarin.

Advertising

2 Comments

  1. To ai itace babbar jahila ko a bible babu auran jinsi kodae dama ita ta hanyar auran jinsin aka sameta ne 🤔🤔🤔

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button