Labarai

‘Yan bingida suna nada kansu a matsayin shuwagabanni a wasu kauyuka da suka kai mamaya suka kwace a jihar Sokoto

Kamar yadda kuka sani ‘yan bindiga sunyi kaurin suna wajan shiga kauyuka tare da aikata mummunar barna a cikin kauyukan, inda suke kashewa al’ummar dake cikin kauyukan sannan kuma su handame dukiyoyin su.

A yau kuma wani laban labari ya bayyana akan ‘yan bindigar inda sukayi juyin mulki a wasu kauyuka dake karamar hukumar sabon birnin jihar Sokoto.

Dan bindiga Bello Turji tate da yaran sa suke suka aikata wannan juyin mulkin a cikin yaran nasa akwai Dan Bakkwallo, Boka I Tamiske, Hassan dan kwaro, Dogo da kuma Jammu Baki.

Sun gayyaci al’ummar dake kauyukan domin zaman tattauwa a tsakanin su wanda al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis 4/10/2021.

Yayin zaman tattaunawar da sukayi da al’ummar kauyukan sun umarci mazauna kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin ‘yan bindigar domin ya zamto hakimin su, inda al’ummar kauyen suka zabi Dan Bakjwallo a matsayayin sabon hakimin kauyen nasu Gamgara.

Nan take Dan Bakkwallo ya gindaya wasu sharuda ga al’ummar kauyen akan cewa, su samar da kasuwanni da kuma masallacai a kauyen nasu.

A wani kauye kuma mai suna Makwaruwa dan bindiga mai suna Boka Tamuske shi da kansa ya data kansa a matsayin hakimin kauyen, sannan kuma yayi kiran gaggawa al’ummar tare da umartar tsohon hakimin kauyen mai suna Dan Sani.

Ya fada masa cewa: Ya sanar da talakawansa da kansa cewa daga yanzu dan bindiga Bika Tamiske ne sabon hakimin su ba shi Dan Sani ba.

Kamar yadda Dailystar Nageria ta ruwaito cewa: A halin da ake ciki a yanzu ‘yan bindigar suke da wuka da nama a cikin wadannan kauyukan.

Muna bukatar ku fadi ra’ayoyin ku akan wannan abin da ‘yan bingigar suka aikata.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button