Sai shugaba Buhari yayi bayani a gaban Allah kan rashin tsaron dake damun jama’ar Arewa, Inji Attahiru Dalhatu Bafarawa
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa yace: Mutanen Arewa maso yamma suna cikin bala’in rashin tsaro, sannan kuma ya bayyana cewa mutane basu da damar kawo kayan amfanin gonarsu gida a yau.
Ya kara da cewa: Mutane suna fama da yunwa sannan an rufe hanyoyin sadarwa da kuma kasuwanni a garuruwa, Tsohon Gwamnan Attahiru Bafarawa ya nemi shugaba Nubari ya dage kan matsalar rashin tsaro.
Attahiru Dalhatu Bafarawa yace: A halin yanzu yankin Arewa maso yamma ana cikin musifa, ya bayyana haka ne a lokacin da gidan jaridar BBC Hausa sukayi shira da shi.
Haka kuma ya koka kan halin da mutanen yankin sa dana shugaban kasa suke ciki, kamar yadda jaridar Vanguard ta bibiyi shirar da aka yi da Attahiru Bafarawa.
Attahiru Bafarawa ya fadi cewa: Sha’anin rashin tsaro wani bala’i ne daya auko mana mutanen da suke wuraren ne kawai zasuyi bayanin halin da ake ciki a Sokoto da Zamfara.
Yace: Abin takaicin shine tsaron kasa yanakan wuyan Gmanatin tarayya ne masu fadawa shugaba Buhari abubuwa suna tafiya daidai, ko suna ce masa da matsala ne?, idan suna fada masa abubuwa suna tafiya daidai ne sun cuce shi kuma sun cuce mu.
Attahiru Dalhatu Bafarawa yace: Allahu (SWT) yasan cewa ana cikin mummunan yanayi a yankin sa na Arewa maso yamma domin jama’a suna kuka.
Ya kara da cewa: Yau naje gida na dawo na shaida da idanuna ba fadamin aka yi ba, mutane sun noma shinkafa da gero amma bazasu iya kaiwa amfanin nasu gida ba.
Duk wanda yahe goma ya dauko kayan amfanin da yasamu bazai koma gida da rai ba kamar Zamfara, an tsare mutane babu waya kuma an rufe kasuwanni.
Da aka tambayi Attahiru Bafarawa cewa: Ko adawa ce tasa yake irin wadannan maganganun sai yace’ lamarin ya shafi har shugaban kasa, kuma Allahu (SWT) zai tambaye shi.
Allah yakawo zaman lfy a nageria
Yes
Allah subhanahu wata ala ya zaunar mana da kasar lfy da zama lfy dan alfarmar MUHAMMADARRASULULLAHI Ameen