Tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta caccaki shuwagabannin Nageriya tare da martani akan tsadar rayuwar da al’umma suke ciki
Kamar yadda kuka sani Mabsurah Isah tsohuwar jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan hausa wato kannywood, sannan kuma ta kasance matar jarumi kuma mawaki Sani Musa Danja.
A yau ne mukaci karo da wani faifai bidiyon jarumar a shafinta na sada zumunta Istagram inda a cikin bidiyon mukaga Mansurah Isah tana korafi akan yadda tsadar rayuwa tayiwa al’ummar kasar Nageriya katutu.
Mansurah Isah ta koka ne akan yadda karancin Man Fetur ya fara wahalar da mutanen jihar Kano, sannan Mansurah Isah tace tabbas tsadar Man Fetur zata kara sanya talakawan Nageriya cikin mawuyacin hali.
Mansurah Isah ta kara da cewa: Tun satin ba yagata wannan karacin Man Fetur din yake faruwa a jihar Sokoto, kamar yadda yake faruwa ga al’ummar jihar Kano.
Jarumar ta kara da cewa: Yau idan ka sayi abu budu kaza gobe idan ka dawo saya sai ka tarar da ya kara duki inda har ta bada misali da Gas tace, idan yau ka same shi budu bakwai gobe zaka same shi budu takwas.
Sannan jarumar ta bada labarin cewa: A kwai lokacin da taje siyan shinkafa ‘yar Hausa amma aka ce mata $Dala ta kara tsada, sannan abin da yabata mamaki shine lokacin da taje siyan rake ta bada Naira dari biyar amma sai aka bata yanka uku maimakin a bata yanka biyar.
Sai ta nuna cewa raken ya mata tsada bisa mamaki sai yace mata $Dala ta kara tsada.
Ga cikekkiyar bidiyon nan domin ku kalla kuji bayanin da tsohuwar jaruma Mansurah Isah tace akan tsadar rayuwar da al’ummar kasar Nageriya suke ciki.
Kalli bidiyon kai tsaye.