Hadiza Gabon da Dan wasan kwallon kafa na Najeriya Shehu Abdullahi sun tofa albarkacin bakinsu akan mutuwar Mahmud Labarina
Shirin Labarina mai dogon zango wanda tashar Arewa24 da tashar Saira Movies suke haska muku a duk sati a wannan lokacin shirin yazo da wani sabon salo, musamman wanda aka haska a wannan satin da yagata.
Kamar yadda kuka sani shirin Labarina a wannan satin da aka haska an nuna cewa Mahmud ya mutu inda mahaifiyar sa da babban bokin sa suka shiga cikin tashin hankali, sannan kuma Sumayya ta bata inda aka nemeta sama da kasa ba’a ganta ba.
Sannan kuma a bangaren Baba Dan Audu wanda ya auri mahaifiyar Mahmud yana ta nuna halin rashin mutunci da kuma rashin imani, inda yasa gaba wajan karfar kudi a wajan masu zuwa gaisuwa.
To a yau kuma muka sami wani faifai bidyon daga tashar Kundin shahara dake kan manhajar Youtube, inda suka wallafa wani labari akan jaruma Hadiza gabon tare da Dan wasan kwallon kafa na Nageriya Shehu Abdullahi.
Jaruma Hadiza gabon da Dan wasan kwallon kasa Shehu Abdullahi sunyi wasu maganganu ne akan mutuwar Mahmud a cikin shirin Labarina, inda suka gabatar da maganganun nasu ta budiyo call.
Ku kalli bidiyon dake kasa domin kuji cikekken labari akan maganganun da jaruma Hadiza gabon da Dan wasan kwallon kafa Shehu Abdullahi sukayi akan mutuwar Mahmud a cikin shirin Labarina.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.