Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Kotu ta kama jaruma Hafsat Idris domin cigaba da shari’ar su da kamfanin UK data gudu musu da kundin aiki

Babbar kotun jiha mai lamba 18 dake zamanta a garin Ungoggo karkashin mai shar’a Zuwaira Yusuf, ta cigaa da shar’arta akan jarumar masana’antar kannywood Hafsat Idris da wani kamfanin Uk Entertainment, akan zargin ta da ake nakin kara sa musu aiki.

Advertising

Wakilin Dala FM Abubakar Sabo ya ruwaito cewa: Kamfanin yana karar jaruma Hafsat Idris ne akan sunyi jinga da ita zata musu wani aiki na TV Show kan Naira Miliyan daya da dubu dari uku, sai dai kafin a kara aikin sai jarumar ta gudu.

Mun sami wannan labarin a cikin wata bidiyo wanda tashar Tsakar gida dake kan manhajar Youtube ta wallafa, inda zakuji cikekken labarin a cikin wannan bidiyon.

kamar yadda dama kun san cewa, a kwanakin baya labarin jarumar ya karade shafukan sada zumunta akan karar da wannan kamfanin na UK Entertainment ya yi kan jaruma Hafsat Idris.

Advertising

Domin kuji cikekken balari sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Advertising

6 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button