Labaran Kannywood

Hotunan Rahama sadau tare da jarumi Sani Musa Danja sun janyo maganganu da cece-kuce

Kamar yadda kuka sani Rahama sadau jaruma ce a masana’antar kannywood wacce tayi fice sannan kuma tauraruwarta take haskakawa, inda jama’a suke tunanin Rahama sadau tafi kowace jaruma fidda sabbin tsaruka da salo kala-kala.

Rahama sadau tayi fice wajan wallafa hotunan jan hankali a shafinta na sada zumunta Instagram wanda jama’a da dama suke bibiyar shafin nata domin kallon hotunan da take wallafa, sannan kuma su tofa albarkacin bakin su akan hotunan.

To a yau ma dai mun leke shafin jarumar inda muka ci karo da wasu sabbin hotuna da Rahama sadau ta wallafa sanye da kayan fulani, a gefenta kuma mukaga jarumin kannywood Sani Musa Danja, inda wannan hotunan suka dauki hankulan jama’a.

Nan take mabiyan jarumar suka fara tofa albarkacin bakin su tare da yaba hotunan da Rahama sadau ta wallafa domin tayi kyau sosai a cikin wannan kayan na fulani, kamar ace itama bafulatanar ce.

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button