Advertising
Advertising
Labarai

Kungiyar Tijjaniyya da Kungiyar Izala zasu hada ka amma bisa wasu sharuda guda 3, cewar Dahiru Usman Bauchi

‘Yan kungiyar Izala da ‘Yan kumgiyar Tijjaniyya zasu hade waje daya amma akan wasu sharuda guda uku wanda babban malamin addini Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gindaya.

Advertising

Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya kasance jagora a Darikar Tijjaniyya ya fadi wata magana wanda ta janyo cece-kuce inda ya bayyana cewa, zasu hada kai da ‘Yam kungiyar Izala amma ya kafa wasu sharuda guda 3, wanda sai ‘Yan kungiyar Izala sun cika su sannan hadin kan zai yiwu.

Kamar yadda kowa ya sani ‘Yan kungiyar Izala da ‘Yan kungiyar Tijjaniyya gaba dayan su musulmai ne sai dai sun sami sabanin fashimta a tsakanin su, inda suka raba kansu akan abubuwa da dama da suka shafi addinin musulinci.

Kuma babban sadanin da ‘Yan kungiyar Izala da ‘Yan kungiyar Tijjaniyya suka sami shine maulidi sabida kusan shine abin da aka fi cece-kuce da maganganu a kai.

Advertising

Amma abin da aka fi ganin shine makasudin raba kan wadannan kungiyoyin shine Bidi’a wato aikata wani abu a cikin addini, wanda Manzon Allah S.A.W da sahabban sa musamman Khalifofin sa basu aikata ba.

To sai dai maulidi yana daya daga cikin abubuwan da Manzon Allah S.A.W tare da sahabban sa basu aikata ba, inda ‘Yan kungiyar Izala suke ganin cewa tun da hakane suna bazasu aikata ba.

Wannan kadan ne daga cikin labarin muhawarar da ake wadannan kungiyoyi guda 2 wato kungiyar Izala da kuma kungiyar Tijjaniyya, zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken labari akan muhawarar da ake.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

One Comment

  1. This is stupidity you brought to us u didn’t itemized the condition brought by Dahiru Bauchi,u only mentioned one difference between ixaala and Darika.But u should atleast listed some condition

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button