Jaruma Hadiza gabon ta wallafa bidiyon malam Isah Ali Pantami a shafin na Instagram wanda ya burge jama’a
Ficacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood Hadiza gabon ta wallafa wata bidiyon Malam Isah Ali Pantami a shafinta na sada zumunta Instagram, wanda hakan yake nuna cewa ya burge ta.
A cikin bidiyon da jaruma Hadiza gabon tawallafa a shafin nata anga Malam Isah Ali Pantami yana wa’azi kan abin da ya shafi rayuwa, yana mai fadin cewa babu wanda ya isa ya kashe mutum sai da yar dar Allah.
Bayan wannan bidiyon ta malam Isa Ali Pantamj da jaruma Hadiza gabon ta wallafa a shafin nata, sai wasu daga cikin mabiyanta suke tunanin ko wannan cece-kuce da jama’a suke akan soyayyar ta da malam Isah Ali Pantami yaje kunnen ta, shi yasa ta wallafa bidiyon nasa a shafinta.
Sannan kuma wasu daga cikin mabiyan nata suna tunanin akwai kamshin gaskiya game da jita-jitar da jama’a suke akan soyayyar ta da malam Isah Ali Pantami, domin gashi a yanzu ta wallafa bidyon sa a shafinta.
To amma a zaton wasu suna ganin kamar bidiyon da malam Isah Ali Pantami yake wa’azi a ciki burge jarumar tayi shi yasa ta dauki bidiyon ta wallafa a shafin tana na sada zumunta domin mabiyanta su gani kuma su karu da abin da yake fada a.
Ga bidiyon da jaruma Hadiza gabon ta wallafa a shafin nata domin ku kalla.