Advertising
Advertising
Labarai

kotu ta yankewa matar da ta azabantar da yaran da take rikewa a hanunta hukunci.

Wata Kotun ta yanke hukuncin cewa, matar ta yi ta zaluntar yaran da suke hannunta sama da shekara uku.

Advertising

A lokacin shari’ar, alkalan sun gano cewa, wadanda Lessels ta azabtar suna fama da ciwo na tsawon lokaci sakamakon zaluncin da ta yi musu.

Laifuffukan sun shafi mutum biyu da aka azabtar wadanda yara ne a lokacin da aka ci zarafinsu, kamar yadda Daily Record ta ruwaito.

Alkali Paul Brown ya ce: “Wadannan munanan laifuffuka ne a kan yaran da ba su da kariya da suke hannun wadda take rainonsu.

Advertising

“Ya kamata wadda ta aikata hakan ta kasance mai amana. Don haka, babu wata makoma ga mai laifin sai gidan yari.”

Wadanda abin ya shafa sun shaida wa alkalan kotun Dundee Sheriff cewa, an nuna wa yaran rashin tausayi yayin da suke hannunta.

A yayin shari’ar ta kwanak uku, wani matashi mai shekara 18, ya ce Rachel ta tilasta masa ya sha amansa bayan ya yi aman abincinsa.

“Ina kuka sai Rachel ta ce za a fitar da ni daga aikin tsarin zamantakewa idan ban sha ba,” inji shi.

Wata wadda abin ya rutsa da ita ta shaida wa kotu wannan lamari sai jikinta ya yi sanyi ta rike kanta don ta kasa numfashi.

A yayin shari’ar, wani wanda abin ya shafa ya ce, Rachel ta ja al’aurarsa, ta tilasta masa dora kansa a kan wani benci, sannan ta sa shi fita tsirara zuwa cikin motarta.

Source: Aminiya

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button