Advertising
Advertising
Labarai

Ni zan fara yin mataimakin shugaban kasa a 2023, cewar Yahaya Bello

Ni zan fara yin mataimakin shugaban kasa a 2023, cewar Yahaya Bello

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce zai
dauki mace ta yi masa mataimakiya idan
jam’iyar APC ta tsaida shi takarar shugaban
kasa a 2023.

Advertising

Bello ya baiyana hakan ne a wani taron
karawa juna sani da yan jarida masu rahoton
labaran siyasa da na kotu a jiya Juma’a a
Abuja.

A cewar Bello, zai baiwa mata muhimmanci
idan har a ka bashi dama ya zabi wanda zai yi
takara da shi.

Gwamnan ya ce ya na da burin yin gwamnati
da 2a ta tafi da kowa, musamman mata,
matasa da masu bukata ta musamman.

Advertising

Ya kara da cewa haka ya ke gudanar da
mulkinsa a Kogi in da bai bar kowa ba wajen
tafiyar da gwamnatinsa.

Bello ya kara da cewa idan ya samu dama, zai
samar da tallafi ga matasa da mata domin
bunkasa tattalin arziki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button