Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ficaccan mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bawa Saratu Daso mamaki a wajan taron bude Gidan Biki da tayi

Kamar yadda kuka sani a jiya ne jarumar masana’antar kannuwood Saratu Daso wacce aka sanin ta da Mama Daso ta bude sabon gidan biki, wanda aka gudanar da gagarumin shagalin biki a gidan tare abokanan sana’arta jarumai Maza da Mata.

Advertising

Sai yau kuma jaruma Mama Daso ta wallafa wani hoton shahararran mawakin siyasa wato, Dauda Kahutu Rarara, tare da yi masa godiya ta musamman akan karamcin da ya nuna mata lokacin daya halarci wajan shagalin bude sabon gidan bikin da aka gudanar.

Jaruma Mama Daso ta fara da cewa: Bazan taba mantawa da karamci da mutuntakar da kayi a Daso Events centre ba, kayimin likin kudi ka bani Dollars ka bawa MC Shahrukan Dollars, da zaka fati a gate a rabawa Securities kudi 50k.

Allah ya saka maka da alkairi, ya kareka daga sharrin makiya.

Advertising

Wannan itace godiyar da jaruma Mama Daso tayiwa shahararran mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a lokacin daya halarci wajan shagalin bikin sabon gidan ta data bude.

Sannan kuma ta sake wallafa wata bidiyo wanda mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana a ciki yana rera waka inda mutane suka kewaye shi suna rawa, wanda har da ita kanta jaruma Mama Daso.

Zamu so mu karbi ra’ayoyin ku akan wannan babban gudun mawar da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yiwa jaruma Mama Daso a lokacin daya halarci wajan shagalin sabon gidan bikin data bude.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button