Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Masha Allah: Jaruma Saratu Daso wacce akafi sani da Mama Daso ta shirya gagarumin biki na bude sabon gidan rato nata mai suna Daso Event center

Jaruma Saratu Daso ficacciyar jaruma ce sannan kuma ta kasance tsohuwar jaruma masana’anyar shirya fina-finan hausa ta kammywood, wanda tauraruwar ta take kan haskakawa.

Advertising

A yau ne muma sami wata wallafa wanda jaruma Daso tayi a shafin ta na sada zumumta Istagram inda ta wallafa wata bidiyon shagalin bikin wani sabon gidan taro data bude mai suna Daso Event center.

A wajan wannan wannan shagalin bikin jaruman masana’antar kannywood Maza da Mata da kuma mawaka sun halarci wajan, domin taya Saratu Daso farin ciki da murna na wannan sabin gidan taron data bude.

Jama’a sun sha rawa sun gwangwaje a wajan shagalin bikin da Saratu Daso ra shirya wanda ita ma tace baza’a barta a baya ba tayi ta tikar rawa, kamar yadda zaku bidiyon a kasa.

Advertising

Bayan wannan bibidyon da Saratu Daso take tikar rawa akwai wasu zafafan hotuna da suka dauka a wajan tare da abokanan sana’ar jarumar masana’antar kannywood, kamar yadda zaku hotunan na kasa.

Bayan nuna murna da farincikin da abokan sana’ar ta sukayi, jaruma Saratu Daso tayiwa kowa da kowa fatan alkairi tare da bayyana farin cikinta akan hadin kan da ‘yan uwa da abokan alziki suka nuna mata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button