Subahanalla: Jami’an tsaro sun kama Amaryar data kashe maigidanta sabida ya kamata da kwarto a gidan sa suna lalata
A yau ne muka sami labari mai cike da abin al’ajabi yadda wata yadda wata matar aure ta kashe mijin ta sabida ya kamata da kwarto a gidan sa.
Mutumin da yana da mata biyu amma ya raba musu gida kowacce tana da gidan ta ita kadai domin samin zaman lafiya mai dorewa, a ranar da wannan al’amarin zai faru mutumin yana dakin Uwargidan sa da kwana wanda kowa yasan idan mutum yana da mata biyu to yana raba musu kwana.
Bisa mamaki sai wannan mutumin ya sami labarin cewa ai wannan Amaryar tasa kwarto yana zuwa wajan ta, amma sabida ya tabbatar da maganar da ake fada masa sai ya tafi gidan Amaryar tasa, da isar sa gidan ta tarar da kwarton a dakin Amaryar tasa nan take yayi nasarar kama shi.
Bayan ya kama kwarton sai Amaryar tasa ta dauko wuka ta cakawa mijin nata sabida kwarton ya sami damar guduwa, sannan tayi kokarin maida al’amarin kamar ‘yan fashi ne suka hari gidan nata amma bata sami damar hakan ba.
A yanzu haka dai Amaryar tana wajan jami’an tsaro domin suna gudanar da cikekken bincike akan al’amarin.
Muna bukatar ku fadi ra’ayoyin ku akan wannan labarin a sashen mu na tsokaci wato comment. Mun gode.