Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wata budurwa tayiwa abokiyar ta tayin auren mijinta inda a karshe tashiga tashin hankali da bakin ciki

A wani labari da muka samu mai cike da abun mamaki da kuma saka ci irin ba mata musammam wanda abin ya faru da ita a cikin wannan laabrin.

Advertising

Wata budurwa mai suna Arewa Queen wanda ta shahara wajan amfani da kafafan sada zumunta na wannan zamani, ya bayyana wani sako mai dake da darasi da kuma wa’azi ga matan da basiyi aure ba.

Shahararriyar budurwar ta bayyana sakon nata kamar haka.

Akwai wata friend dina abu kadan sai tace nazo na auri mijin ta. Sai nayi murmushi na share, aka dauki lokaci muka sake haduwa ta sake gaya mun haka …nayi mata yake sabida abun ya soma bani haushi. Ana nan na taba biya mata muka je kasuwa tare dai nan muka dawo ruwan sama ya tsareni a gidanta har mijin ya dawo.

Advertising

Nan take ta kasa sukuni ta dameni mu koma dakinta , nace mata ni gida zani , tunda ruwan ya tsagaita , aikuwa sai ga mijin da sauri ya fito wai bari ya ajeni nace ya barshi kawai nan fa ya kafa naci. Ita kuma ta tamke fuska tamau, nikam na tsaya Ina kallon ikon Allah , habawa nan fa ya dauki Leda ta yayi gaba , na tsaya nayi tsuru , can dai nace mata sai munyi waya ta amsa da “Uhum.

Ina zuwa naga ya zuba kayana a baya bance komai ba na bude gidan gaba na zauna , yaja mukayi gaba , ya isheni da surutai nayi shiru, aikuwa Yana zuwa kofar gidan mu yace nabasa number ta nayi shiru yace walhy bada wata manufa zai amsa ba nasake yin shiru.

Ya zaro wayarsa ya latsa sai ga wayata na ringing yace mun tunda naki bashi tawa to ga nasa nan nayi saving , ai number ta ta kai shekara a wayarsa ya jima da samun number na.

Na sake shiru sabida kawai tuna attitude din matarsa nake yi na dazu . Ya bude central lock na fito na bude baya na jawo kayana nayi gaba.

Arewa Queen tace: To ni dai bansan mai ya faru ba na daina ganin Sadiya a status ashe blocking dina tayi, mijin ke gaya mun ashe ranar sunyi tashin Hankali da ya koma wai don me yake rawar kafa a kaina.

So na yakeyi ko mene, nan dai har yayi barin zance ya ce bari ya kira ni ta tambayeni Idan da wani abu tsakanin mu nan fa tace atafau a ina ya samu number wayata Idan ba soyayya mukeyi ba.

Kai chakwakiya dai iri iri, ni Ina gefen guda baiwar Allah na qare mun zagi, gulmace gulmace iri, banbi takai ba na cigaba da sabgogin gabana. Shima mijin nata na gasa masa aya a hannu ya gaji da yawo da hankalin da nake masa ya rabu dani.

Ta kara da cewa: Ni kullum abun da ke dauremin kai har yau tasan tana da Irin wanna kazamin kishin dacan take cewa na auri mijin ta ko tsabagen cin fuska ne irin na matan yanxu Idan sunga sunyi aure ke bakiyi ba sun dunga jefama mutun magana cikin magana oho … ni Shiyasa kawaye mata basu dameni ba I hate drama.

Sadiya In Sha Allahu sai Hamza ya maki kishiya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button