Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Bayan Jarumi Nuhu Abdullahi yayi shira da BBC Hausa akan tarihin rayuwar sa wani ya karyata shi akan abubuwan daya fada

Daga Ishaka Usman Wali.

Advertising

Zuwa ga jarumi Nuhu Abdullahi wanda akewa lakabi da Mahmud a shirin Labarina mai dogon zango.

Usman Wali ya fara da cewa: Nayi matukat mamaki irin yadda na kalli shirar da kayi da BBC Hausa a shirin nan nasu na daga bakin mai ita a inda suka so suji tarihin ka rayuwar ka.

Kai kuma sai ka nuna musu cewar an haifeka a garin Kano kayi makarantar Primary da Secondary duk a jihar Kano, hakika naji babu dadi sakamakon irin yadda ka juyawa kauyenku baya sabida yanzu rayuwar ka taci gaba kuma nayi mamaki matuka.

Advertising

Ina so wadanda suka kalli shirar da BBC Hausa tayi da Nuhu Abdullahi susan cewa, an haife shi ne a wani kauye da ake kira tudun bichi a karamar hukumar danko wasagu dake jihar Kebbi.

Nuhu Abdullahi yayi Model Primary School a tudun bichi inda ya zarce zuwa garin wasagu domin ya shiga makarantar Secondary School mai suna “GOVERNMENT ARABIC AND ISLAMIC SECONDARY WASAGU, a lokacin da marigayi Malam Jafaru yana Principal inda Malam Abubakar na Diri yake Mataimaki.

Nuhu Abdullahi shine House Captain a wasagu House inda shi kuma abokin sa mai suna Habibu Random yake House Captain a Sakaba House, ya sanni na san shi domin kanin sa Aliyu Abdullahi abokina na ne kuma mun kwana a daki daya da shi Nuhu Abdullahi.

Lokacin da ina sabon shiga Makarantar akwai wani Prefect mai suna Tijjani a Garba kanin matar yaya na ne shine wanda ya dauke ni ya kai ni Prefect Room na rinka kwana a can duk da ba House di na bane, domin ni ina dauko House ne wanda Nura yake jagoranta.

Nuhu Abdullahi ya sha aiki na na debo masa ruwa a bokiti idan zanyi wanka da kuma sauran dawai niya da yake sakani sakamakon nine yaro kuma Junior a dakin, dalilin da yasa ban sha wata wahala ba kenan sabida sun shaku da duk wani Prefect na kamarantar.

Bayan ana shirin gina Masallaci ne Nuhu Abdullahi ya dan sami sabanin fashimta da Malam Abubakar na Diri Vice Principal wanda shine yayi sanadiyyar barin sa makarantar a lokacin da yake gab da rubuta Junior Waec.

Imda ya koma Lagos da zama wajan yayan sa mai suna Abdurrahaman wanda shine yayi sanadiyyar shigar sa harkar Fim, a can ne yaci gaba da karatu wanda har Allah ya taimake shi ya kammala Jami’a.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button