Advertising
Advertising
Labarai

Wani matashi ya mutu yayin da mahaifin sa ya mika shi hannun ‘yan bijilante domin su hukunta shi akan ya masa laifi

Wani mata shi mai suna Haruna Allah ya karbi rayuwar sa a hannun ‘yan bijilante yayin mahaifin sa mai suna Auwal Ado ya mikashi domin suyi masa hukunci mai tsauri sabida ya gagari mahaifin nasa.

Advertising

Wannan al’amarin ya faru ne a kahyen Kafin Gana dake karamar hukumar birnin Kudu dake Jihar Jigawa.

Mahaifin Haruna wato Auwal Ado yana zargin dan nasa ne da satar Masara a gonakin mutane sabida ransa ya baci ya kama shi inda ya mika shi ofishin ‘yan bijilante domin su hukunta shi.

Bayan ya mika shi hannun ‘yan bijilante din daga nan suka masa mummunan hukunci ta hanyar yi masa gwale-gwale, daga nan kuma al’amari ya baci inda aka mika shi asibita amma sai yace ga garin ku nan rai yayi halin sa.

Advertising

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Gidawa ASP Lawan shisu Adam ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda yake tuni suka kama mahaifin yaron wato Haruna wanda ya rigamu gidan gaskiya, tare da wani mutumi wanda za’a yi bincike sosai akan al’amarin.

Sannan kuma yayi nasiha ga ‘yayan yara dasu rika yiwa ‘yayan su hukunci mai sauki koda sun aikata musu wani mummunan laifi, domin gujewa faruwar al’amari irin wannan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button