Bayani akan wasu jaruman kannywood 4 wanda Allah ya jarabce su da mummunan ibtila’i a rayuwar su
Jarumi Tijjani Abdullahi Asase wanda aka fi sanin sa da Tijjani Asase wanda a yanzu yake jagorantar wannan shirin mai dogon zango “ADUNIYA”, wannan jarumin ya kwashe tsawon shekaru sama da ashirin a masana’antar kannywood.
Sannan duk wanda yasan fina-finan da wannan jarumin yake fitowa yasan fina-finai ne na daba barkwanci da sauran su, a yanzu haka shine ya gabatar da wannan shirin mai dogon zango “ADUNIYA” wanda shirin ya sami karbuwa a wajan jama’a.
A shekara ta 2017 jarumi Tijjani Abdullahi Asase shima Allah ya jarrabce shi da gobara wanda tayi sanadiiyar konrwar gidan sa gaba daya, wanda ko tsinke ba’a fitar ba daga abubuwan dake cikin gidan.
Sai dai Allah ya kubutar da iyalansa babu wanda yaji rauni ko wani abu makamancin haka, dunbin jaruman masana’antar kannywood sun jajatan nasa tare da yi masa addu’ar Allah ya mayar masa da abin da aka rasa.
Wannan labari mun same shi daga tashar Arewapackage wanda take kan dandalin manhajar Youtube inda suka yi bayanin jaruman daya bayan dayawanda Allah ya jarabce su da wani mummunan ibtila’i a rayuwar, inda zakuji cikekken bayanin a cikin bidiyon dake kasa.
Jaruman da Allah ya jarabce su da wannan mummunan ibtila’in a rayuwar su, su budu ne akayi bayanin nasu amma wasu daga cikin su zaku iya sanin su wasu kuma ba lallai ne ku sansu ba.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani akan wadannan jaruman na kannywood wanda Allah ya jarabce su da mummunan ibtila’i a rayuwar su.
Allah ya kiyaye