Dawowar Jaruma Rahama Sadau masana’antar kannywood da wani sabon salo ya janyo mata cece-kuce da maganganu
Jama’a da dama masu kallon shirin fina-finan hausa suna tambaya aka cewa wai shin Jaruma Rahama Sadau ta dawo kannywood ne, tun bayan da aka wallafa wasu hotunan Jaruma Rama Sadau a gurin daukar wani sabon Fim mai suna Gambo Da Sambo.
Wanda ake daukar Fim din a garin Gombe wanda a cikin shirin Fim din akwai Jaruman masana’antar kannywood irin su, Rabi’u Daushe, Rahama Sadau, Magaji mijin yawa, Sani Musa Danja.
Jama’a da dama sunayin tambayar ne sabida ganin wannan sabon shirin Fim din da ake dauka a wata Jiha daga Jihohin Arewa tare da wasu Jarumai na masana’antar kannywood, shin ko Jaruma Rahama Sadau ta koma masana’antar kannywood domin ta cigaba da harkar Fim dinta.
Sanin kowa ne abin daya faru da Jaruma Rahama Sadau a wata shakara data gabata inda ake ta dambarwa tsakanin Jaruma Rahama Sadau da sauran abokan sana’arta tare da al’umma masoya Annabi Muhammad (S.A.W), akan wasu kaya data sanya a jikinta cikin rashin sa’a sai aka sami wani katon kafiri fajiri dan wuta ya taba martabar Fiyayyan halitta Annabi Muhammad (S.A.W), a kasan wannan hoton nata data wallafa a shafinta.
A wannan lokacin abin da Jaruma Rahama Sadau tayi janyo mata cece-kuce da kuma tada kura wanda har kungiyar shirya fina-finan hausa wato Moppan suka bayyana cewa, an dakatar da Jaruma Rahama Sadau.
Bayan haka sai Jaruma Rahama Sadau ya bayyana a cikin wata bidiyo tana kuka tare da bada hakuri da neman yafiya da al’ummar Musulmai masoya Annabi Muhammad (S.A.W, sannan kuma ta bayyana cewa bada masaniyar hakan ta wallafa wannan hoton nata ba.
Amma sai tace, ta dauki wannan laifin tunda ita ce silar faruwar wannan al’amarin sannan kuma ta tuba tayi alkawarin haka bazata sake faruwa ba nan gaba.
Amma har kawo yanzu babu wanda yaji wata sanarwa da aka yi akan cewa an janye korar da aka yiwa Jaruma Rahama Sadau, wanda ita kuma Jaruma Rahama Sadau ba wanda ya sake ganin ta a cikin wani shirin Fim tun lokacin da wannan al’amarin ya faru.
Ko shirin ta wanda take haskawa a tasharta ta Youtube mai suna ‘Yar Minista shima ta dakatar da shi bata sake haskawa ba tun da aka tsaya a kashi na 8.
Ku kalli wannan bidiyon dake kasa domin kuji cikekken balari akan dawowar Jaruma Rahama Sadau masana’antar kannywood.