Advertising
Advertising
Labarai

Subahanallah: Asirin wani matashi ya tonu wanda yake aikata mummunar farna akan su Allah ya shirya

A yau mun dami labari akan wani mutu wanda yake yaudara ‘yan mata yana guduwa musu sa wayoyin su na hannu, kamar yadda tashar Kundin shahara ta wallafa bidiyon da aka kama mutumin ake tuhumar sa.

Advertising

Wata baiwar Allah ce takai korafin mutum akan wannan mummunan halin nasa inda take cewa, wani saurayi yaje har gidansu sannan ya nuna mata yana santa wanda har ma ta sanar da iyayan.

Bayan nan kuma ashe wannan mutumin ya lura fa wayar da take hannun wannan matar sai yace zai sauya mata wannan wayar ya saya mata babba, inda take ganin abin kamar wasa sannan yake mata wace waya ce tafi ta kowa girma a gidan su sai tace ta kaninta.

Nan take yasa ta dauko wannan wayar kanin nata ta kawo masa inda ya rike wayoyi guda biyu a hannun sa, daga nan sai yacewa matar ai ya nemi makullin motar sa ya rasa sabida haka yana bukatar su taya shi budawa.

Advertising

Sai matar tace dama yana da mota ne sai yace mata eh amma ya ajiye ta a bakin titi sannan yace a cigaba da duba masa makullin motar sa, yayin da suka sunkuya suna duba makullin motar shi kuma sai ya sani wani lungu ya tsere da wannan wayoyin.

Amma a yanzu haka jam’an tsaro sunyi nasarar kama shi inda ake tuhumar sa akan wannan satar wayoyin da yayi, kamar yadda zaku cikekkiyar bidiyon kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button