Labarai

Innalilahi wainna ilaihir raji’un: Allah ya yiwa mutumin da yake shirin Angwancewa da matar sa kwanan nan rasuwa a hatsarin mota

A yau ne muka sami labarin wani mutumi wanda Allah ya karbi rayuwar a lokacin da yake shirin zama ango da wata shahararriyar ‘yar kasuwa mai suna Rafeeah Zirkarnain.

Matar da zai aura mai suna Rafeeah Zirkarnain ita ce ta fara wallafa labarina a shafinta na sada zumunta Facebook da misalin karfe bakwai 7:00 da daddare a ranar Alhamis, inda tayi wallafar kamar haka.

Innalillahi wa Inna ilaihir raj’iun masoyi na Sani Ruba ashe baza mu kasance mata da mijin ba a ranar 11 ga watan Disamba Tun jiyan nake jin wani yanayi a raina amman na rike tunanin a raina bazan taba samun mutum irinka a matsayin miji ba, kamar yadda ta wallafa a shafin nata na Facebook.

Masoyin nata mai suna Sani dan shakara 36 wanda yake zaune a garin ruba dake jihar Jigawa daga nan kuma ya koma garin Jos Jihar Filato.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa: Mutumin mai suna Sani ya gamu da ajalin nasa ne a wani hatsarin mota daya ritsa da shi a kan titin numan zura dake Gombe a ranar Alhamis.

Wata majiya tayi kokarin jin ta bakin matar da mutumin zai aure amma abin sai taki basu hadin kai domin taki daga duk wani kira da ake mata ko sakwannin da ake tura mata, tayi hajan ne sabida tana cikin dimuwa da firgici akan abin daya faru da masoyin nata.

Kafin mutumin ya rasu yayi karatun sa a bangaren koyar da aikin jarida a Jami’ar Bayero dake Jihar Kano (BUK), inda tuni mutane da dama ciki har da malaman Jami’ar suka tura sakon ta’aziyyar su ga iyayan mutumin da kuma matar da zai aura.

Muma a matsayin mu na masu wannan shafi “Hausadailynews” muna rokon Allah yaji kan sa yasa aljanna ce makomar sa, idan namu tazo Allah yasa muma mucika da imani. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button