San zuciya yasa jarumin kannywood Garzaki Miko ya aikata irin abin da mawaki Davido ya aikata ga masoyan sa
Kamar yadda kuka sani shahararran mawakin nan na kudancin Nageriya wato Davido ya saka wata gasa wanda masoyan sa suka yi turo masa kudade, domin nuna kauna a gare shi.
Bayan wannan gasar da mawaki Davido yasa wanda masoyan sa suka turo masa kudade, sai kuma wani labari ya bulla na jarumin masana’antar kannywood wato Garzali Miko inda shima ya sanya wannan gasar ga masoyan sa domin su turo masa kudi.
Inda jarumi Garzali Miko ya wallafa wannan labarin a shafin sa na sada zumunta Instagram, inda yake cewa.
Gaskiya da za’a yimin abin da aka yiwa Davido wallah da naji dadi sosai.
Lokacin da jarumi Garzali Miko ya wallafa wannan labarin a shafin sa na sada zumunta sai kuma mabiyan sa suka sake ganin wani sabon sako wan ya wallafa yana mai cewa.
Masoyana ina godiya da kuka ce naturo account number ta :02549283832 Gt bank
Mikailu Garzali ina alfahari da ku masoyana.
Bayan wallafar sabon sakon da yayi a shafin nasa nan take wata masoyiyar sa ta fara turo masa Naira budu uku 3 N3000.