A Gaban idanun mu ni da Mahaifiyata aka zare ran dan uwana, cewar Aliko Dangote
Daga karshe shahararran dan sakuwar nan mai kudin Afirka Aljaki Aliko Dangote ya magantu akan mutuwar kanin sa Alhaji Sani Dangote, daga comr Abba Sani Pantami.
Marigayi Alhaji Sani Dangote wanda shine mataimakin shugaban rukunin Kamfanonin Dangote ya rasu a ranar Lahdi 14 ga watan Nuwamba a kamar Amurka bayan jinyar da ya sha fama da ita.
Wanda ya karbi jagorancin Jam’iyyar All Progressives Congrass “APC” Asiwaju Bola Ahmad Tunubu a gidan sa dake Jihar Kano a ranar Juma’a 19 ga watan Nuwamba, Aliko Dangote yace mahaifiyar su da yaran sani na a wajan da aka dauki ran marigayin.
Ya ce ya fi masu radadi a lokacin da likitoci suka fada masu cewa dan uwansa na da kimanin awa daya da yayi masa saura kafin ya mutu, Daily Trust ta rahoto.
Aliko Dangote ya kara da cewa: yaji radadi dan uwan nasa ya mutu a gaban sa kuma a gaban mahaifiyar su da kuma wasu yara.
Dangote tace: Shi da kan sa saida yaji zuciyar sa tayi rauni a lokacin da yake ganin ran dan uwansa yana fita daga jikin da.
Sannan kuma yayi godiya ta musamman ga Bola Ahmad Tinubu akan ziyarar da ya kai masa inda yake cewa, yaji dadin dangar takar sake tsakanin su da ahalin Bola Ahmad Tinubu na tsawon lokaci.
Aliko Dangote ya kara da cewa: Rashin tabbas da mutuwa take da shi shi yasa ako da yaushe ake so a kullum mutum ya rinka yin abin alkairi, sannan yace yadda mutane suke ta zuwa wajan ta’aziyyar abu ne mai ban mamaki amma hakan zai taimaka musu wajen rage radadi mutuwar.
Sannan yace musamman a gareni sabida mun taso tare, amma abin da min zafi sosai lokacin da suka fada mana cewa nan da ‘yan sa’o’i dan uwana zai mutu kuma dole mu kalli yadda numfashin sa na karshe zai fita.
A sakon ta’aziyyar Bola Ahmad Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dan Lagos kuma babban dan Kasar Nageriya, Tinubu ya kuma bayyana cewa kudi baya siyan rai kuma babu abun da mutum zai iya yi idan lokaci yayi.
Sannan kuma Bola Ahmad Tinubu Ya yi kira ga iyalan marigayin da su dauki hakuri da ci gaba da yi masa addu’an samun dacewa.