An bayyana wasu daga cikin jaruman Kannywood wanda suka taimakawa Jarumi Sani Garba SK da kudade domin ceton rayuwar sa
Da duk mai kallon shirin Fin-Finan Hausa na Masana’antar Kannywood yasan cewa, a yanzu haka jarumi Sani Garba SK yana fama da rashin lafiyar da kowa ya ganin shi sai ya tausaya masa, inda aka sami wasu daga cikin abokan sana’ar sa Maza da Mata suka taimaka masa da wasu kudade.
Jarumi Sani Garba SK yana fama da wasu cututtuka da suke damun sa sannan wanda har ma aka bayyana cututtukan da suke damun sa sune kamar haka, Ciwon suga da kuma Ciwon Hanta.
Idan bazaku manta ba a kwanakun baya jarumi Sani Garba SK ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake neman taimakon al’umma akan wannan jinyar da yake fama da ita, domin a taimaka masa da wasu kudade da zai yi amfani da wasu wajan yiwa kan sa magani.
To a wannan lokacin kuma sai muka samu wani bayani daga Shafin Fauziyya D Suleiman wanda shugaba ce a Kungiyar Nan Ta Creative Helping Needy Foundation (CHNF), wato Kungiyar Taimakawa Gajiyayyu Da Marayu.
Inda ta bayyana wasu daga cikin jaruman Masana’antar Kannywood wanda suka taimakawa Jarumi Sani Garba SK da wasu kudade domin yayi amfami da dasu wajan sayan magani da kuma sauran abubuwa.
Yanzu haka abdulamart mai_kwashewa ya Bashi Dubu Dari biyar 500k domin a kai shi asibiti, sannan Jaruma Hadiza gabon ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin 250k , sai kuma Jarumi Ali Nuhu ya bashi Dubu Dari 100k.
aeeshatsamiya_backup ta bayar da Dubu Dari 100k sannan akwai mutane da yawa da suka taimaka masa wanda suma a cikin Masana’antar Kannywood sukeke, kuma muna rokon Allah ya saka musu da alkairi akan wannan taimakon da suka yi.
Sannan Fauziyya D Sulaiman ta kara da cewa: Kamar yadda muke fada muku ciwon Jarumi Sani Garba SK ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, amma kuma al’umma dan uwanku ne musulmi Wanda wannan ‘yan uwantakar ta fi ta sana’a za ku iya taimak masa ba tare da cin mutuncin kowa ba.