Jarumin shirin Izzar so Lawan Ahmad ya aika sakon abin kunya ga masoyansa kamar yadda Ado Gwanja da Garzali Miko suka yi
Kamar yadda kuka sani Lawan Ahmad ficaccan jarumi ne kuma jagaba a cikin shirin mai dogon zangon wato Izzar so wanda yanzu haka shirin ya sami karbuwa a wajan miliyoyin mutane na Arewacin Nageriya.
A cikin shirin Izzar so ana kiran Jarumi Lawan Ahmad da Umar Hashim wanda ya sami daukaka daga wajan jama’a da dama, sannan kuma ya sami sabbin mabiya a shafin sa na sada zumunta Instagram.
Jarumi Lawan Ahmad ya wallafa wani dan gajeren rubutu a shafin sa na sada zumun Instagram inda yake cewa.
Nima yau inason cin albarkacin Annabi Muhammad s.a.w Ga account number 2119215122 UBA Bank Nagode.
Ganin wannan wallafar da jarumi Lawan Ahmad yayi nan take masoyan sa da abokan arziki suka fara tura masa kudin da ya bukata a wajan su, kamar yadda mawakin Kannywood kuma jarumi wato Garzali Miko ya wallafa irin wannan sakon a shafin sa na sada zumunta.
Amma nan take wasu mutanen suka fara tsokaci akan wannan wallafar sakon da jaruman suke yi a shafukan su na sada zumunta, akan mabiyan su da sauran jama’a suka tura musu kudi, inda suke ganin hakan kamar toko ne.
Duk wannan wallafar da jaruman suke na cewa suna bukatar a turo mudu kudi ta biyo baya ne lokacin da wani shahararran mawakin Nageriya mai suna “Davido”, ya wallafa wani dako a shafin na sada zumunta domin yana bukatar duk wani masoyin sa ya tura masa da kudi.
Wanda har ficaccan Mawakin masana’antar Mannywood Ado Gwanja ya kura mada da Naira dubu goma 10K.
Inda bayan wannan lokacin wasu daga cikin Jaruman kannywood suka fara irin wannan wallafar a shafukan su na sada zumunta domin jama’a suna tura musu kudi, kamar yadda masoyan mawaki “Davido” suka masa.