Advertising
Advertising
Labarai

Subahanallahi wata Budurwa ta kashe kanta sabida wata hatsaniya data auku tsakanin ta da saurayin ta

A wani roho ta da Blueink Hausa suka samu daga Jami’ar Umaru ‘Yar adu’ dake Jihr Katsina kan cewa, wata Dalibar makarantar ta sha guba sakamakon wani dan safabi da ya shiga tsakanin su da Saurayin ta.

Advertising

Kamar yadda majiyar ta bayyana cewa: Ana zaton wannan budurwar da ta kashe kanta ‘Yar aji uku 3 ce a sashen Nazarin Zamantakewa wato “Sociology” a jami’ar.

Majiyar ta kara da cewa: Saurayin Dalibar da shima tsohin Dalibi ne a Jami’ar wanda ya kammala karatun sa Bara, ya yanke hukunci ne kan cewa zai rabu da Budurwar tasa shi yasa ita kuma ta dauki wannan matakin kashe kan nata.

Sai dai wasu bayanai sun tabbatar da cewa: Tun daran ranar Juma’a Dalibar take asibitin Jami’ar amma kamar yadda wasu bayanan suka bayyana cewa, an sake mayar da ita wata asibitin dake cikin garin Katsina.

Advertising

A wasu rahotanni da suka bayyana sun ce: Dalibar da tasha maganin kashe kwari ne wato “Instecticides” inda wasu kuma suka ce, tasha “Septol” wasu ma na cewa “Sanitizer” Tasha, wasu na cewa “Fiya Fiya” Tasha, an sami rahotanni daban-daban akan abin da ta sha wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button