Advertising
Advertising
Labarai

Wata Yarinya ta aikawa da Mahaifinta wani sako wanda kowa yayi mamakin abin da Yarinyar ta rubuta a cikin sakon

Labarin wata Yarinya mai cike da abin mamaki ya karade kafafan sada zumunta domin jama’a da dama sunyi mamakin wasikar da Yarinyar ta aikawa da Mahaifinta akan wata bukata da take nema daga gare shi.

Advertising

Ga dai yadda sakon Yarinyar ya fara kamar haka.

Assalamu Alaikum Abba ya office Allah ya taimaka ya dafa maka yayi jagora, dama Abba shawara ce dani sau 2 ina yin jamb ba naci yanzu ana Shirin in sake ta 3, Baki nayi ba a maimakon haka me zai hana abawa Abdul dama tunda ya shirya inyaso nayi can, kamar yadda Walida Aminu da Surayya Jafar suke duk suna karatu.

Bayan haka sai Yarinyar ta kara da cewa.

Advertising

Nafara sanarwa da Aunty Aysha tace ba ruwanta sannan Umma Kuma ta falfaleni da fada bayan haka sai yaya Kuma ya zazzageni, Abba Allah yasa zaka fahimceni ka dubeni da idon basira.

Wannan yarinya hakika tayi tunani mai kyau Kuma tayi abinda ya dace da Alama dai gidan su yarinyar irin ‘yan Bokon nan ne masu akida, to amma Allah yasa Mahaifin nata ya fahimceta kamar yadda ta ambata.

Wannan sako da Yarinyar ta aikawa da Mahaifin nata da yawan mutane sun mamaki sosai duba da irin tunanin da tayi wajan rubuta wannan sakon, sannan kuma ta aikawa da Mahaifin nata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button